Wata babbar kotu da ke zaune a Abuja ta sauke wasu yan majalisar dokoki ta jiha su 20 daga muƙaminsu bayan sauya sheƙa daga jam;iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Ƴan majalisar dokokin jihar Cross River su 20 sun sauya sheƙa daga tsohuwar jam’iyyar su ta PDP zuwa jam’iyyar APC a shekarar 2021 da ta gaba.

Alƙalin kotun Justice Taiwo Taiwo a zaman kotun na yau ya sauke ƴan majalisun daga mukaminsu bayan sauya sheƙa da su ka yi daga jam’iyyar da aka zaɓe su a cikin ta.

Tun da farko jam’iyyar PDP ce ta shigar da kara gaban kotun inda ta buƙaci kotun ta sauke ƴan majalisar 20 daga muƙaminsu bisa sauya sheka daga jam’iyyar da mutane su ka zaɓe su a cikin ta.

Idan ba a manta ba jam’iyyar PDP ta shigar ta ƙara wasu  ƴan majalisar jihohi da na wakilai da wasu ƴan majalisar dattawa da gwamnan Zamfara a gaban kotu domin ganin an sauke su daga muƙamansu.

Jam’iyyar na ikirarin cewar muddin aka zaɓi mutum a cikin jam’iyyar to ƙuri’ar da aka zaɓe shi mallakin jam’iyyar ce don haka su ke buƙatar kotun ta sauƙe mutanen da su ka sauya sheƙa tare da maye gurbinsu da wasu da jam;iyyar ta amince da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: