Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya ce ƴan bindiga a jihar na iko da ƙananan hukumi 12 daga cikin 25 na ƙananan hukumin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci ƴan gudun hijira wanɗanda su ka rasa muhallinsu a sanadiyyar hare-haren ƴan bindiga da kuma ambaliyar ruwa.
Ya ƙara da cewa, jamj’an tsaro na ƙoƙarin aiwatar da sabbin hanyoyi domin ganin an kawo ƙarshen ƴan bindigan.

Gwamnan ya ce akwai mutane sama da dubu huɗu waɗanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a sanadiyyar aikin da ake yi a dam ɗin Zungeru.

Gwamnan ya kuma ziyarci ƙaramar hukumar Munya sannan ya gana da ƴan sa kai tare da alƙawarta musu cewar gwamnatinsa za ta samar musu da sabbin makamai don yaƙi da ƴan bindiga.