Sama da mutane miliyan guda ne za a raba wa katin zaɓen su waɗanda su ka yi rijistar tun da farko.

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta ce ta shirya tsaf domin fara bayar da katin zaɓe ga masu su waɗanda su ka fara yin rijistar a farko.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce za a fara bayar da katin zaɓen a mako mai zuwa.

Hukumar ta ce mutanen da su ka yi rijista daga ranar 28 ga watan Yunin zuwa ranar 30 ga watan Disambar shekarar da ta gabata.

Mutane 1,854,859 aka kammala wa aikin rijistar katin zaɓen a faɗin Najeriya kuma za a fara bayarwa a mako mai zuwa.

Sai dai hukumar ta sanar da cewar wajibi ne wanda ke da alhakin katin kaɗai shi za a bai wa katin ba tare da ya aika da ɗan saƙo ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: