Labarai
TETFUND – Farfesa Sulaiman Bogoro shi ne ya maye gurbin AB Baffa Bichi – Mujallar Matashiya


Bayan sauke shugaban Tetfund Baffa Bichi an maye gurbinsa da farfesa Sulaiman Bogoro, a safiyar yau ne dai gwamnatin tarayya ta bayyana sauke tsohon shugaban tetfune ɗin.

Rufda ciki da faɗa da wasu daga cikin mukarraban gwamnati na daga cikin dlilan da suka sa aka sauke Gwamnatin tarayya ta sauke shugaban kula da cigaban manyan makarantun jami a a kasar.
Ana zargin Dakta Abdullahi Baffa Bichi da wawure wani kaso mafi tsoka da ake tunanin na daga cikin bitalmanin gwamnatin inda yake wadaƙa da su a harkokin siyasa.

Wani makusancinsa da muka zanta da shiya bayyanawa mujallar Matashiya cewar, akwai da yawa daga cikin kudaden da ake zargin ya babbake wanda kuma yake kashesu sake babu kaidi.

AB Baffa dai na nuna yatsa da wasu daga cikin ministocin kasar nan tare da kyakkyawan zaton cewar ana zaman doya da manja da gwamnatin Kano.

Idan ba a manta ba ma ko da a baya gwamnatin jihar kano na zargin AB Baffan da yi mata gadar zare wanda hakan ya kara karfin zargin da akewa tsohon shugaban kula da manyan makarantu da jami a na ƙasar.
Labarai
Tsadar Karatu Na Iya Sa Rabin Ɗaliban Jami’a Su Gudu – ASUU


Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta ce kashi 50% na ɗaliban da ke karatu na iya ajiyewa saboda tsadar karatu da ake ciki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa ɗaliban da ke karatu a jami’o’in ƙasar kashi 50% daga ciki na iya ajiye karatun nasu.
A wata hira da aka yi da shugaban a gidan talabiji na Channels ranar Lahadi da daddare, ya gargaɗi ɓangaren ilimi na ƙasar da su farga a kan abinda ka iya faruwa.

Sai dai ya alaƙanta ƙara kuɗin da jami’o’i su ka yi da mafi ƙarancin albashin da ake biya na naira 30,000 a ƙasar.

Sannan ya ce akwai hatsari mai yawan gaske idan aka samu ƙarin matasa masu yawa da su ka bar makaranta.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙarawa malaman jami’a albashi da kashi 30 ga masu matsayin farfesa.
Labarai
Gobara Ta Kama A Kotun Ƙoli Ta Najeriya A Abuja


Rahotanni daga baban birnin tarayyar Najeriya Abuja na tabbatar da cewar kotun ƙoli ta kama da wuta.

Ofishin alƙalai uku aka ruwaito sun ƙone bayan tashin gobarar.
Godan jaridar Arise ya ruwaito cewar, wutar ta kama wai ɓangare na cikin kotun.

Sai dai ba a san sanadin tashin gobarar ba.

Wannan dai itace gobara da aka yi a kusa-kusa wadda ta shafi ofishin gwamnati.

Ko a watan Mayun shekarar da mu ke ciki, gobara ta kama a rundunar sojin samar Najeriya.
Yayin da a shekarar da ta gabata ta 2023 ma’aikatar kuɗi ta tarayya wani ɓangare ya kama da wuta.
Labarai
Amuruka Ta Gargaɗi Ƴan Ƙasar Mazauna Najeriya Kan Ziyartar Wasu Jihohi Har Da Kano


Ƙasar Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su kiyaye wajen ziyartar wasu jihohi da ka iya faɗawa cikin hatsari.

Sanarwar na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike da su ka gano an samu ƙaruwar aikata manyan laifuka a jihohin.
Jihohin sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Kogi, Bauchi, Kaduna, Kano, Gombe, Bayelsa, Rivers, Enugu da jihar Bayelsa.

Sauran jihohin su ne Imo, SokOto, Zamfara, Katsina, da jihar Abia.

Ƙasar ta gargaɗi mutanenta da su kiyaye wajen ziyartar waɗannan jihohi domin su na iya faɗawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane ko wasu miyagun laifuka.

Binciken da su ka yi sun gano cewar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na amfani da ƙarin mutane a wasu sassa domin cimma muradinsu.
Sannan gwamnatin Amurukan ta buƙaci ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su ƙara sanya idanu a kan dukkanin zirga-zirgarsu don gudun faɗawa hatsari.
-
Mu shaƙata8 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Labarai6 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Girke girke5 years ago
YADDA AKE LEMON SHINKAFA