Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ko ku daina ko kuma ku bar Najeriya, ɗaurin shekaru 15 ga duk wanda yake luwaɗi – saƙon Ƴan sanda ga Ƴan luwaɗi

Kakakin ƴan sanda shiyya ta biyu Dolapo Bodmos ta buƙaci masu ɗabi ar neman maza a Najeriya da su bar ƙasar ko kuma fuskantar tsattsauran mataki.

Bodmos wadda ta buƙaci ƴan ƙasa waɗanda suke da hujja a kan ƴan luwaɗi komai ƙanƙantata da su gabatar da ita a gaban ƴan sanda don ɗaukar matakin shari a.

ta bayyana cewa duk wani mai neman maza ya sani cewa Najeriya ba ƙasar zamansa bace, kamar yadda kundin tsarin mulki yayi tanadin ɗaurin shekaru sama da 15 ga duk wanda aka kama.

Ta ce babu wata doka da ta hana kama wanda yake da rigirta da masu luwaɗin haka kuma duk wanda aka kama da hannu cikin ƙungiyar zai fuskanci hukunci.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: