Yadda aka zaɓo Naziru har ya       zama Sarkin waƙa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya naɗa Naziru Ahmad a matsayin sarkin waƙarsa.

Naziru Ahmad dai ya kasance mawaƙi da a yawa lokuta ke karkata ga masu sarauta.

An zaɓoshi ne ganin yadda ke waƙarsa cikin tsari tareda yanayi na al ada.

Naziru sarkin waƙa na yin waƙoƙi ne waɗanda suka sha bambam da na sauran mawaƙan hausa na zamani.

Yana yiwa kansa kirari da sarkin waƙa ne tun kafin a naɗashi sarkin waƙa, cikin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust ta yi da shi ya bayyana cewa bai san dalilin da ya shigar da shi sana ar waƙa ba, sai dai ya taba mafarkin ya zama mawaƙi tun lokacin yana shekara 7 a duniya.

Cikin tattaunawar ya ce lokacin da ya fara waƙa babu ɗakin waƙa wato STUDIO sai dai ya rera a gaban mutane.

A cikin shekarar 2000 kuwa, sarkin waƙa Naziru ya fara shiga waƙar ka in da na in.

Ko da aka tambayeshi menen dalilin da ya sa ya karkata kan waƙarsa yanayin gargajiya?

Nazir Ahmad ya ce yana yin hakan ne ganin yadda da yawan mawaƙa ke tsayar da kansu kan zamani zalla, kuma yana da kyau a ce mawaƙa na ɗabbaƙa yanayin waƙa irin nazamanin baya kamar shata da ɗan kwairo, sai dai hakan na da wuya ganin yadda rubutawa da rera waƙar ke  buƙatar nazari, har ma yake tunanin hakan ne ke hana sauran mawaƙan ɗaukar salonsu.

A cikin tattaunawar an tambayeshi ko shin zargin da ake na yin soyayya da jaruma Hadiza Gabon gaskiya ne?

Ya ce tabbas haka ne, kuma suna ƙaunar junansu amma ba su tsayar da lokacin da za su yi aure ba Allah ne masani sun muƙa al amuransu gareshi.

An naɗa Naziru sarkin waƙar sarkin Kano ne a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll, a ranar 27 ga watan Disambar da ya gabata.

Manyan jaruman fina finan hausa kamar Ali Nuhu, Sadiƙ Sani Sadiƙ da sauran mawaƙa maza da mata ne suka samu halartar bikin naɗin bayan da aka yi walimar cin abinci a daren ranar har ma mujallar Matashiya ta hango Ado Gwanja a wajen.

One thought on “Yadda Naziru ya zama sarkin waƙar sarkin Kano – Matashiya”
  1. Hello. I have checked your matashiya.com and i
    see you’ve got some duplicate content so probably it is the reason that you don’t rank high in google.
    But you can fix this issue fast. There is a tool that
    rewrites content like human, just search in google: miftolo’s tools

Leave a Reply

%d bloggers like this: