Majalisar dattawan ƙasarnan sun dakatar da zaman da za tayi a kan sauke alƙalin alƙalai na ƙasar nan.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da kakakikin majalisar ya fitar a yau wanda suka buƙaci a gabatar musu da wasu takardu da suka shafi doka kafin zaman.
Tun bayan sauke alƙalin alƙalan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Ibrahim Tanko a matsayin mai riƙon kujerar alƙalan.
An sauke tsohon alƙalin alƙalan ne bisa ƙin bayyana wasu kadarorinsa kafin fara aiki a ofishinsa.
A wani labarin kuma ana cigaba da zanga zanga kan nuna ƙin amincewa da cire tsohon alƙalin alƙalan Najeriya karanta a nan https://matashiya.com/2019/01/28/346/


