Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Yadda aka ƙona gidan ɗan takarar gwamnan kano na jam’iyar PDP

Tun a jiya daddare rahotanni suka tabbatar da ƙona gidan ɗan takarar gwamnan kano Abba kabir yusif na jam’iyar PDP.

Wasu matasa ne da ba’asan ko suwaye ba suka cinnawa gidan wuta inda ya ƙone ƙurmus kafin.
Gidan ɗan takarar gwamnan dake unguwar chiranchi a ƙaramar hukumar gwale an maida shi ofishin jam’iyar PDP wanda hakan ya bawa matasan damar ƙone gidan.
Zuwa yanzu dai ƴan jam’iyar PDP sun tabbatar da zargin cewa ƴan jam’iyar hamayya ce ta APC suka kai wannan hari ofishinsu.
Har yanzu dai babu labarin asarar rayuka sai dai dukiyoyi ciki harda ƙona wata mota ƙirar Golf 3.

Dama dai ƙaramar hukumar gwale cike take da rikici na siyasa kasancewar ɗan takarar gwamnan PDP a ƙaramar hukumar yake, sannan kuma shugaban jam’iyar APC ta jihar kano Abdullahi Abbas shima a nan yake.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: