Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran ƙasa

Za a sauya shugaban INEC na ƙasa

Akwai yuwuwar sauya shugaban hukumar zaɓe na ƙasa bayan ɗage zaben da aka shiya yi yau a Najeriya.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa matuƙa kan ɗage zaɓen wanda ya bayyana hakan a matsayin gazawar aiki da hukumar zaɓen.

Shugaban ya koma Abuja a yau bayan zuwansa mahaifarsa don gudanar da zaɓen da aka shiya yi yau a baya.

Mujallar Matashiya ta gano cewar da yawan mutane ba su fita ba a yau, kasuwanni sun kasance a rufe, da sauran wurare da dana.

Farfesa Mahmud Yaƙub dai ana tunanin maye gurbinsa da shugabar hukumar ta riƙo Amina Zakari.

Sai dai hukumar zaɓen ta ƙasa ta bayyana cewar ta ɗage zaɓen ne bisa dalilai da suka shafi tsaro da kuma rashin kai kayan zaɓe ofisoshin hukumar a kan lokaci.

Wannan al amari dai ya janyo cece kuce a faɗin ƙasar kasancewar an samu sanarwar ne a cikin dare.

Da yawan mutane sun shirya gudanar da zaɓe a yau hasali ma ma aikatan zaɓen da aka ɗauka na wucin gadi sun halarci wurin wanda wasu suka kwana a can duk da muku ukun sanyi da ake yi a wasu jihohin ƙasar.

Shin kuna ganin sauya shugaban hukumar zaɓen zai haifar da ɗa mai idanu?

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: