Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Dole INEC ta yi aiki sahihi tunda mun basu duk abinda suke buƙata

Cikin kalaman shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayin zaman gaggawa da aka yi yau a Abuja ya bayyana cewar an bawa hukumar zaɓe dukkan abinda suke buƙata.

Ya ce wajibi ne ta fito ta yiwa al umma jawabin ɗage zaɓen da ta yi gudun zubewar mutuncinta a ison duniya.

Shugaba Buhari dai ya kira taron gaggawa ne a yau bayan da hukumar zaɓe ta ɗage ranar zaɓe zuwa 23 ga watan nan maimakon 16 ga wata.

A nasa ɓangaren shugaban jam iyyar APC na ƙasa Adam Oshimole ya buƙaci a yi tankaɗe da rairaya cikin hukumar zaɓen ta INEC.

Ya ce abin kunya ne a ranar da za a fara zaɓe su bayyana ɗage zaɓen bayan an kallama shiri tsaf.

Sai dai itama babbar jam iyyar hamayya wato PDP ta zargi jam iyyar APC da hannu cikin ɗage zaɓen, wanda suka bayyana cewar shiri ne na yin maguɗi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: