Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Yadda na fara gyaran jannareto – wata Budurwa a Kano

Fadila Sani Shu’aibu ƴar jihar Kano a ƙaramar Hukumar Fagge ta bayyana cewar sha’awa ce ta sakata yin sana’ar wadda a yanzu ta zamto mata madogara.

Tun bayan da ta koyi gyaran jannareton a ofishin mujallar Matashiya yayin da suke bayar da horon sana’o’I ga matasa kyauta, ta ce bayan ta kammala ta ƙudiri aniyar buɗe wajenta tare da yin sana r a farashi mai sauƙi.

“Bayan na kammala koyon sana’ar tawa ne kuma na buɗe wajena tare da ɗaukar wasu nima ina koya musu.

Ƙalubalen da nake fuskanta na yadda wasu           mutanen ke ɗaukata ban san me nake ba, wasu   kuma su ƙi bawa sana’ar tawa muhimmanci amma wannan bai sa na gaza da abinda na sa a raina ba” inji Fadila.

“Da yawan mutane na ɗauka cewar kamar ban iya ba amma idan suka zo sai su tabbatar, wannan sana’ar kuma tawa ta yimin komai tunda ina biyan buƙatuna da ita”  a cewarta.

Matashiyar budurwar wadda ta rungumi sana;ar gyaran gyannareto, ta bayyana cewar sai da ta kammala karatunta na fannin malunta wato NCE amma ba ta tsaya sai ta yi aikin gwamnati ba sai ta zo koyon  sana’ar gyaran jannareto bayan da ta ji an sanar mujallar Matashiya za su bawa matasa horo kyauta.

Ta sha alwashin cigaba da riƙe sana’ar tata wanda ta ce tana da burin bunƙasa ta ta zama babban kamfani da zai ke gyara jannareto kuma ko da ta zama wani abu a cikin sana ar ba zata yar da ita ba.

Sannan ta shawarci matasa da su kasance masu dogaro da kansu ba sai sun tsaya bin kyale-kyale ko aikin gwamnati b, domin akwai sana’o’I da yawa waɗanda za su zama tsani zuwa ga cika muradin kowanne mutum.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: