Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da kama Rashida Said Muhammad wadda ake zarginta da hankaɗo mijinta daga bene yayin da ta jiyoshi yana waya da budurwarsa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan cikin ƙunshin takarda da ya rabawa manema labarai a yau.
Ya ce Bayan da rashida ta ji mijin nata yana waya da budurwarsa, sai ta yi ƙoƙarin kwace wayar don ganin da wa yake wayar, al amarin da ya sakata amfani da wannan damar har ta hankaɗo mijin daga bene kuma ya faɗo ƙasa warwas har ma ya ce ga garinku nan.

Mijin nata mai suna Adamu Ali ya rasa ransa bayan da aka kaishi asibiti.

Kakakin ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya ce ƴan sanda na cigaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su miƙata gaban ƙuliya don girbar abinda ta shuka.
Mujallar Matashiya ta gano cewar, da yawan mata sun hallaka mazajensu a baya wasu kuwa sun nakastasu a sanadin kishi.