Shugaban Majalisar Dattawa kuma, Sanata Bukola Saraki ya taya ƴan takarar da suka samu nasara a zaɓe da ya gudana a Jihar Kwara murna tare da yi musu fatan alheri.
Wannan saƙon ya biyo bayan Sanatan ya musanta taya wanda ya kayar da shi na Jam’iyyar APC a zaben Mazabar Danmajalisar Dattawa ta Tsakiyar Kwara, Dr. Ibrahim Oloriegbe murnar lashe zaben a jiya Litini. Amma yanzu wannan ya tabbata.
Saraki ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter. Ga abin da ya rubuta:
“Ina yi wa ɗaukacin ƴan takarar da suka yi nasara a zaɓe a faɗin Jihar Kwara fatan alheri, bisa ayyukan cigaban al’ummarmu da za su sa a gaba.
Fatana shi ne Al’ummar Jihar Kwara su samu ayyukan cigaba daga kowwace gwamnati a dukkan matakai na.ƙasa, Nagode


