Ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya na jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gudanar da taron manema labarai a Abuja,inda ya bayyana cewa sakamakon babban zaben da aka bayyana tamkar Almara ce kawai kuma ba zai amince da shi ba.
Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar najeriya ne, ya yi takarar shugabancin kasar ne a karkashin jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye a hannun Shugaba mai-ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Atiku ya ce; A matsayinsa na ɗan Nijeriya yana ganin wannan zaben da aka gudanar zamba ne cikin aminci da INEC ta gudanar, ba shi da ingancin da zai samar wa ƴan Najeriya shugaban ƙasa domin ba ra’ayinsu ke nan ba.
Ya kuma bayyana dalilin rashin amincewa da sakamakon kan cewa ƙuri’un da Buhari ya samu a wasu ɓangarorin ƙasar sun wuce ƙima, ciki har da jihohin kudu maso kudu da kuma na Arewa maso gabas waɗanda suke fama da rikici a yankin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: