Cikin wani faifan bidiyo da ɓangaren yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Buhari da ma jam iyyar APC suka saki, mujallar Matashiya ta ga shugaban ƙasa Buhari na kira ga al’umma da su fito su zaɓi jam iyyar APC a zaɓen gwamnoni da ake tinkara ranar asabar.

Shugaba Buhari dai ya bayyana cewar, a baya ya samu matsaloli ganin yadda aka yi zaɓen tumun dare, sai dai a wannan lokaci ya bayyana cewar zaɓar ƴan jam iyyar APC ɗin ne zai bashi damar cigaba da ayyukan da ya fara kamar samar da tsaro da dai sauransu.

A ranar asabar 9 ga watan da muke ciki ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar jiha da ke faɗin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: