Rahoton da muke samu yanzu yanzu an kama wasu ƴan mata guda biyu suna shiga gida gida suna siyan kuri’un mata a mazabar gama kwanar yan daru.

Ƴan matan suna shiga gidaje ne suna bada kuɗi 5000 ko 3000 su karɓi katin zaɓensu.
asirinsu ya tonu bayan da aka gano su nan take matasa suka far musu da duka, yanzu haka an antafi dasu zuwa Ofishin ƴansanda ta gwagwarwa domin binciken lamarin
Kamar yadda wakilin Mujallar Matashiya ya rawaito mana, sannan kuma ya zanta da wasu wanda abin ya faru a idonsu da wani mai suna Rabiu Musa Haruna shaidun gani da ido, ya tabbatar mana da gaskiyar al’amarin, ya ƙara da cewar ɗaya daga cikin matan gidansu ta shiga domin gudun tsira, shima anasa bangaran mahaifinsa mallam Musa Haruna, ya shaidama matar bata fita ba daga gidansa saida jami’an tsaro suka zo suka fito da ita. Idan. Ba’a manta ba akan wannan mazaɓar ta gama ne aka samu hatsaniya inda mataimakin gwamanan kano Nasiru yusif Gawuna da kwamishinan ƙananan hukumomi,Murtala sule garo da Shugaban ƙaramar hukumar nassarawa Lamin sani suka tada hatsaniya a wurin tattara sakamako har takai ƴan sanda sukayi awon gaba dasu wanda takai ta kawo faɗan sakamakon wanda ya lashe zaɓen jihar kano ya gagagara.

