Wani matashi Bashir Sharfaɗi ya bayyana cewar saura ƙiris ya fara bayar da darasu a kafar yanar gizo, wand za a samu dukkan bayanan da ake buƙata cikin harshen Hausa.

Sharfaɗi matashi mai shekaru 22 a jihar Kano ya fara sana arsa a yanar gizo tun bayan da ya yi yunƙurin buɗe gidan rediyo mai zaman kansa.

Cikin wata zantawa da mujallar Matashiya tayi da matashin, ya bayyana cewar a halin yanzu yana yin sana arsa kuma yana samun riba mai yawa ta hanyar yanar gizo, haka kuma yana da burin ƙarasa makarantar da ya fara assasawa wadda za a ke yin darrusa cikin harshen hausa.

‘Nafuskanci ƙalubale mai tarin yawa, amma daga baya mutane sun fuskanceni har ma idan na kira mutum don gudanar da bincikena sai ya ke murna” inji Sharfaɗi.

Bashir shafaɗi ya ja hankalin matasa da su ke yin amfani da yanar gizo dama kafafen sada zumunta bisa ƙa’ida don samun ribar da ke cikinta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: