Bahaushe na cewa Inda Ranka kasha kallo, tabbas abin haka yake, don kuwa gashi Wani Abin Al’ajabi ya faru, inda wata mata haifi ƴan biyu, sai dai kuma bincike ya tabbatar Kowanne da Ubansa.
Matar ƴar ƙasan chana da ba’a bayyana sunanta ba ƴar kimanin shekaru 30,ta haifi jariranta biyu sai dai a lokacin da ake ƙoƙarin yi musu Rijista, bayan anyi musu Gwajin DNA sai masu binciken suka gano yaran basu da alaƙar cewa ubansu ɗaya.
Sai dai matar ta bayyana cewa ita namiji ɗaya ne yake saduwa ta ita, kuma basu yi auri ba.
Yanzu haka dai kallo ya koma sama a Asibitin da matar ta haihu.


