Mataimakin Shugaban kasa Yemi Oisinbajo, ya bayyana cewar Gwamnatin tarayya na ciyar da dalin ban Firamare kwai miliyan shida da dubu dari takwas da kuma yanka musu shanu guda 598, sannan kuma daliban na lamushe dakwalen kaji ɗai ɗai har 138,000 a duk mako.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a Legas lokacin da yake gabatar da takarda a jami’ar Legas a bikin da take karo na 50 na yaye dalibai da suka kammala karatu.