Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bada umarnin gaggawa na dakatar da haƙar ma adanan albarkatun ƙasa a jihar Zamfara.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da runɗunar ta yi kuma aka rabata ga manema labarai.
Sannan an umarci dukkan ƴan ƙasashen wajen da ke yankin da su ƙauracewa wajen.

