Yanzu haka hankalin Al’umma ya karkata kan da wata batun fallasa da ta kunno kai a tsakanin wasu fitattun jaruman masana’antar Kannywod, Hadiza Gabon da Amina Amal, inda Amal ta ke zargin Hadiza Gabon ta na neman ta,ta hanyar Maɗigo.

Zargin ya samo asali ne tun lokacin da Jaruma Amina Amal ta sanya wasu hotunanta a shafin ta na Instagram da ke nuna tsiraici, hakan yasa ita kuma Hadiza Gabon ta nuna rashin jin daɗin abinda Amal ɗin tayi, sannan ta buƙaci ta cire su daga Instagram, ita kuma Amina Amal sai ta fusata da wannan shawara ta Gabon inda ta maida mata da martani na cewar ta fita hanyar ta, sannan ta bayyana cewar Gabon ta dade tana sha’awar yin lalata da ita ta hanyar Maɗigo, har ta sanya tattaunawar da suka yi da Hadizan inda take lallaɓata da suje su huta na ƴan kwanaki a wani hotel.

Waɗannan kalamai na Amal sun matuƙar harzuka jaruma Hadiza Gabon, inda ta yi nasarar ritsa Amal din ta kalubalance ta akan ta kawo hujjar ta cewa ta taɓa yunkurin yin fasiƙanci da ita.
Sai dai daga baya Amal ta ƙaryata kanta da cewar bakomai bane ya janyo faɗin hakan face aikin Shaiɗan da ƙwaya suka sa ta yin waɗannan kalamai ga Hadiza Gabon
Sai dai itama hadiza Gabon ta fallasa yadda Amal ke bata labarin cewar tana samun gamsuwa a lokacin da maza ke saduwa da itane idan ta tuna da Gabon ɗin, wacce ta daɗe tana mata nasiha da ta riƙa kame kanta a matsayin ta na ƴa Mace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: