Sojojin Najeriya masu fatattakar ƴan garkuwa da mutane tare da satar shanu a Zamfara sun cafke Mataimakain shugaban ƙaramar hukunar Anka bisa zargin haɗin bakinsa wajen garkuwa da mutane.

Rundunar sojin ta ce bayan garkuwa da mutane Yahuza Wuya na da hannu wajen satar shanu da cefanar da su.
A wani binciken sirri da hukumar ta ce ta yi ta gano Yahuza na da hannu a ciki kuma ta cafkeshi don gudanar da bincike.

