Wata ta aiko da tambaya cikin shirin rabin ilimi da mujallar Matashiya ke gabatarwa cewa menene hukuncin yin biki wanda ya haɗar da Party, Dinner, Kanu kafin ɗaura aure.

Mallam Muhammad Tukur Moriki ya ce matuƙar al’ada ta zo kuma ba ta yi karo da addini ba, babu laifi yin hakan kafin biki ko bayan biki.
Sai dai abin dubawar shi ne, me ake yi idan an ce wajen? To wannan wajibi a faɗa haramun ne idan ya haramta in kuma babu laifi to babu makawa za a iya yin bukukuwa kafin ɗaura aure da kuma bayan an ɗaura aure.

