Adam zango wanda jarumi ne a masana antar Kannywood ya kuma angwancewa da amaryarsa sofiyya a can jihar Kebbi.

Wannan shi ne karo na 6 da jarumin yake angwancewa.

Ya rabu da mata biyar ciki har da uwargidansa da ma amaryar da ya aura a baya bayan.

Da yawan mata na nuna rashin jin daɗinsu ganin yadda yake gwani a fagen soyayya musamman a fim, sai gashi ya zamto mai auri saki kamar yadda wasu ke bayyanawa.

Adam Zango ya bayar da sanarwar ɗaurin aurensa inda daga bisani ya bayyana cewar an ɗage zuwa wani lokaci, amma daga bisani aka ɗaura auren kamar yadda ya bayar da sanarwar farko.

An ɗaura auren a ranar Juma ar da ta gabata kuma har yanzu bai bayyana dalilinsa na yin kwan gaba kwan bayan da ya yi a baya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: