Babbar kotun jiha da ke zaune a Ungogo ta bayyana naɗin sabbin sarakunan da aka yi a Kano a matsayin tatsuniya.

Kotun ta bayyana hakan ne yayin zamanta na yau bayan da wasu suka shigar da ƙorafi kan naɗin sarakunan har ma kotun ta dakatar da bikin basu sandar mulki.

Tuni dai majalisar dokokin jiha ta yi doka kuma ta rattaɓa hanu tare da samun sahalewar Gwamna Ganduje bisa sabuwar dokar ƙarin sarakuna huɗu a wasu yankunan na jihar.

An dai naɗa sarakunan ne kamar haka Sarkin Gaya, Sarkin Ƙaraye, Sarkin Bichi da Sarkin Rano sai sarkik cikin Gari Mallam Muhammadu Sanusi ll.

Yanzu dai kotun ta ce babu wasu sarakuna a Kano illa sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll kaɗai ta sani a matsayin sarkin duk gari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: