WAI ME YA SA ‘YAN NAJERIYA, su ke karyar cewa kasar su Kasa ce mai tarin arziki ne? -Daga Abdullahi Isah.

Wannan tambaya ce da na dade ina yi amma har yanzu ban samu wani da ya bani hujja da za ta sa in amince cewa NAJERIYA kasa ce da ta ke da dumbin arziki ba.
Idan kana hira da dan kasar nan game da halin da kasar nan ke ciki abu na farko da zai ga ya ma; ‘wallahi ba don shugaban nin mu ba, da yanzu kasar nan ta ci gaba kamar Amurka ko Ingila’ kai da jin wannan zance ga mai hankali kasan maganar bance ce marar tushe.

Idan ka tambayi mai wannan tutiya cewa menene arzikin da kasar nan ke da shi? Kafin ka rufe baki zai baka amsa ‘Man fetur’, shi a zaton sa kasar da ta ke da man fetur’ ta fi kowace Kasa arziki a duniya kuma kamata ya yi ta fi kowace kasa ci gaba a duniya.

Kafin in yi nisa kan wannan batu zan dan koma baya kan wani irin wannan muhawara da mu ka yi da wani bawan Allah a shekarar 2005 lokacin ni kaina ina da karancin shekaru sosai gaskiya to amma na fuskanci wani lamari da masu shekaru da suka fi nawa suka kasa fahimtar haka.
Abinda ya faru bawan Allah nan cewa ya yi NAJERIYA kasa ce da tafi kowace kasa a duniya arziki, dana tambaye shi arzikin me NAJERIYA ta ke da shi da ta fi kowace kasa a duniya; wato bawan Allah nan da ya fusatan kamar ya dakeni waini da nake yaro me nasani shi fa Malamin tattalin arziki ne a daya daga cikin makarantun Sakandire da ke Kano.
‘Ya ci gaba da cewa, Man fetur’ din Najeriya ba don ana sace kudin da shugabanni ke yi ba wallahi da yanzu mun kai Japan’.
Tabbas jama’a da ke wajen kusan duk sun yarda da abinda ya ce saboda hujjar cewa ni yaro ne bansan komai ba kuma shi Malamin Tattalin arziki ne.
Bayan ya gama hayaniyar sa sai nace to ai wannan lamari ne mai sauki shin jimillar nawa Najeriya ta samu wajen sayar da Man fetur’ a shekarar da ta gabata? Da muka bincika sai da ta kai mu ga aikawa da tambaya a gidan rediyon BBC inda bayan mako 2 aka karanta wasikar, aka yi hira da wani jami’in kamfanin NNPC Wanda ya tabbatar da cewa Najeriya ta samu zunzurutun kudi har dala biliyan 20, abin al’ajabi a ranar aka kuma bayyana a wannan gidan rediyo cewa a birnin Mumbai kawai, kasar Indiya ta samu dala biliyan 20 akan harkar ICT.
Wannan amsa da labarin ya kawo karshen tutiyar da ya ke yi kan arziki da kasar ke da shi.
Amma abin takaici har yanzu har gobe matasa na kasar nan da dama da masu ilimi da marasa ilimin suna ci gaba da tutiyar cewa ai kasar su arzikin da ta ke da shi ya wuce gaban wasa.
Allah sarki mai iko, masu fadin wadannan kalamai ba su san cewa idan za ka sayar da arzikin Man fetur’ na Najeriya kaf din sa gaba daya akwai manyan kamfanoni a duniya da ba zai iya sayan maka su ba.
Misali kamfanin Apple darajar kamfanin ya kai dala tiriliyan daya, Wanda adadin tun fara hakar mai a Najeriya a cikin shekara ta alif da dari tara da hamsin kasar nan ba ta sayar da man da ya kai haka ba.
Jama’ar kasa ta sun kasa gane cewa ilimi ne arziki ba albarkatun kasa ba shi ya sa manyan kasashe da suka fi ci gaba irin su Amurka, Ingila, Faransa, Japan, Italiya, Canada, da Jamus duk ilimi ne ya kai su matsayin da suke ta bangaren kere-kere da bincike na kimiyya.
Kasar China da Indiya duk sun dau turbar ci gaba kuma dukkannin su ilimi ne ya kai su.
Idan man fetur shine arziki me ya sa kasashe da dama a afurka kasafin kudin su ya fi na Najeriya? Me ya sa kudaden da suke samu a shekara ya fi wadda Najeriya ta ke samu?
Wannan lokaci ne da ya kamata matasan mu su farga su tashi su nemi ilimi, gwamnatoci kuwa su zage dantse wajen bunkasa bangaren ilimi.