Babbar kotun ƙoli da ke zamanta a Babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen ɗan takarar jam iyyar PDP.

Ƙorafin da abokin takararsa Jafar Sani Bello ya shigar, Alƙalin kotun ƙolin babban jojin tarayya Tanko Muhammad ya jagoranta, ya ce hukuncin da kotin tarayya ta yanke a baya yana bisa ƙa ida.

Yayin mayar da kalamai bisa hukuncin kotun Abba Kabir ya nuna kwarin gwiwarsa bisa nasarar da ya samu, wanda ya ce za su tabbatar da aikin demokaraɗiyya matuƙar buƙatarsu ta biya.

Sanarwar wadda ta fito da sa hannun kakakin Abba Kabir Sunusi Bature ya nuna matsayin da suke a yanzu shi za su samu a mataki na gaba.

Haƙƙin mallaka Mujallar Matashiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: