Hukumar JAMB ta cimma matsaya inda ta amince da maki 160 ne zai bawa ɗalibai damar shiga jami a ta gwamnati.

Bayan zaman da hukumar ta yi da masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a jihar Osun hukumar ta jamb ta ce maki 140 aka cimma matsaya wajen bawa ɗalibai damar shiga jami ar da ba da gwamnati ba.
Haka kuma maki 120 ne zai bawa ɗaliɓai gurbin shiga makarantun kimiyya da fasaha na gwamnati yayin da aka cimma matsaya don bawa ɗalibai gurbin karatu a makarantun kimiyya wadda ba da gwamnati ba waɗanda suke da maki 110.

Da alama dai ɗalibai a bana za su samu gurbin karatu a jami o i da sauran makarantu.

(C) mujallar Matashiya