Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yau Alhamis a zauren majalisar Dattawa.
A baya dai, Hukumar Zaɓe ta ƙi ba Okorocha Satifiket ɗin zaɓe bisa zargin ya Tilasta wa baturen zaɓe da ya bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara ta karfin tsiya.
Sai dai tun a wannan lokaci, Okorocha ya ƙi amincewa da zargin hakan ta sa shi garzayawa kotu.
Bayan sauraren ƙarar, kotu ta yanke hukuncin cewa INEC ta tabbata ta mika wa Okorocha Satifiket ɗin sa, saboda baturen zaɓe ne kawai yake da ikon bayyana wanda yayi nasara da wanda baiyi ba.
Kuma ya bayyana Okorocha a matsayin wanda yayi nasara a zaɓen.
Wannan Umarnin Kotu yasa Tilas INEC ta mika masa Satifiket din ranar Talata sai dai ta ce zata ɗaukaka ƙara kasancewar bata amince hukuncin kotun ba.


