Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake naɗa Abba Anwar a matsayin dakataren yaɗa labaran gwamnatinsa.

Abba Anwar dai ya kasance Sakataren yaɗa labaran gwamnan tun a kusa da ƙarshen zangon mulki na farko.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kaɓo Alhaji Usman Alhaji ya rattaɓawa hannu, Abba Anwar dai zai cigaba da zama a kujerarsa ta sakataren yaɗa labaran gwamnatin Kano.

Abba Anwar dai ya kasance ɗan jarida wanda ya yi aiki da jaridar Guardian kafin zamansa sakataren yaɗa labaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: