Wasika ga kwamishinan yansandan jihar Kano…

Bayan dubun gaisuwa da kyakyawan Fatan
alheri da addu’ar Allah yasa a gama lafiya nake
rubuta maka wannan budaddiyar wasika
domin ankarar dakai akan batun binciken matar nan da suka yi fada da mijin ta har fadan ya baci.
A gaskiya ana neman yin tuya amance da albasa, domin ni a fahimtata wannan al’amari fa rikici ne ya turnuke tsakanin miji da mata a cikin daki su kadai, har takai rikicin ya zama dauki ba dadi ta hanyar amfani da makami wajen kai hari da kare kai.
Daga maganganun su masu fadan na fahimci cewar an yi dambe a tsakani su, har takai an samu zubar da jini da kumburar mukamiki da kurjewar wasu sassa na jiki, rikici ne dai Wanda takai an sami casualties.
Har yanzu babu Wanda zai iya bayyana hakikanin abin da ya faru don hakan binciken ‘yansanda cikin tsanaki shine zai warware gaskiya a gane mahari da Wanda aka kaiwa hari, a fahimci Wanda aka kaiwa farmaki da kuma Wanda ya kare kansa, amma a yanzu a iya cewar magana ce ta kokawa a tsakanin mutum 2, Wanda bisa adalci su biyun ya kamata a kama a tuhume su da laifin tarzoma da tayar da husuma daga bisani a bambamce Wanda yafi laifi ko a sulhunta su a yafi juna ko kuma a kaisu kotu, To amma ya mai girma Kwamishina a yanzu naga ita matar kawai aka kama, domin shi mijin yana kwance a asibiti kuma naje banga ‘yansanda na gadinsa ba saboda kar ya arce, tunda a ka’ida ya kamata ace yana karkashin bincike akan tuhumar aikata laifi. Ya mai girma Kwamishina, kyale mijin tare da cigaba da tsare matar tamkar barin jaki ne ana barin taiki, ya kamata a dauki matakin da ya dace gudun kada mata suce kuna nuna musu wariya, ya mai girma Kwamishina, duk d
sanda mutane 2 suka yi fada ko wani ya kai kara duk biyun ake kamawa ace sun yi 2 fighting amma ga cikakken 2 fighting har an yi kare jini biri jini, amma yansanda sun kama sashe daya sun bar gudan, koda yake bansani ba ko nan gaba za a kamo daya barin. Babban abin da muke bukata shine adalci, a tsakanin kowa, amma yin haka zai kashe gwiwar mata suga kamar yansanda sun fi son kama mace idan tayi dauki ba dadi da namiji.
Allah ya bayyana gaskiya, Allah ya taimaki rundunar yansandan jihar Kano mai albarka.
Wasalam ka huta lafiya.

Nasiru Zango

Nagode maka Nasir zango. Wannan Shine batu na gaskiya.