Karen farauta
Bismillahirrahmanirrahim Allah ka tsaremu mugun ji da mugun gani
Babbar barazanar da ke illa cikin ruwan sanyi bai wuce yadda masu amo da kwarwa ke ƙasƙantar da kansu a gaban bayin talakawa ba.
Muddin za a cigaba a haka babu shakka babban naƙasu da koma baya na tafe cikin al umma.
Kamar yadda na ji cewa cikin rukunin mutanen da suka jajirce aka tabbatar da ƴanci a ƙasa sune tsani na huɗu da babu abinda zai yuwu sai da su, sai dai a shiga rigarsu don biyan buƙatar waɗanda ke da maiƙo a jikinsu.
Haƙiƙa akwai abubuwan ban mamaki da ban haushi wasu lokutan ma sai mutum ya kyalkyala dariya idan haushi ya ƙure ganin cewa mutanen da ke da dama sun zubar da ita suna damalmala hannu cikin bagiren da ba za su samu daraja ba bayan sun dawo ga al umma.
Ko da yake an ce hatimin nasara ya fi daraja ga mutunci amma ga masu hankali sun san cewa hakan tsantsar gangan ce da babu birkin tsayawa a daidai.
Babban abin takaici ne ganin yadda ake amfani da wasu daga cikin mutane masu daraja don biyan buƙatar wasu ko da yake akwai wasu masu zaman kansu da ake samun oganninsu a shaƙa musu naira su kuwa su tirsasa na ƙasansu don cimma burin mutane ƙalilan da za su amfanar da kansu ba al umma ba.
Sanin kowa ne yadda aka ringa yaɗa labarai na gangan tare da amfani da manyan kafafen yaɗa labarai wajen ƙirƙirar labarai ko kambama abu don cimma burin wani ɓangare a siyasa, haƙiƙa hakan illa ce babba a nan gaba.
Bari na taƙaita, abinda zai faru a ƙarshe shi ne za a samu gurɓatattun mutanen da za su hanaku cin kuɗin da kuka karɓa ko kuka kwasa, idan kuka dawo cikin mutanen kuka gujesu tun a farko ba za ku yi mutunci ba.
An ɗaukeku tamkar masu kawo wahayi amma a wannan lokaci an shiga shakku kan zantukan da kuke yaɗawa tunda idan mutum bai yi taka tsantsan ba sai ya afka mawankar Ƙuliya.
Tunda ko da a yanzu baku da mutunci da daraja a idon wancananka saboda sun san abinda kuke ƙullawa, ba wata barazana ta faɗar gaskiya da za ta tinzirasu tunda dai kun.zubar da ƙima da mutuncinku a idonsu.
Amma har yanzu ba a makara ba za a iya ɗaukar gaɓaran gyara don samun nasarar aikin a nan gaba.
Abubakar Murtala Ibrahim
28/06/2019

Leave a Reply

%d bloggers like this: