Hukumar hisbah ta jihar Kano ta ce Tana rarraba dakarunta Zuwa sassan da aka ware domin lamuran da Suka shafi aikin hajji don ganin an gudana cikin nasara.

Babban daraktan hukumar Mai barin gado mallam abba saidu Sufi shine ya bayyana hakan ga manema labarai yace hukumar ta Saba irin wannan aikin duk shekara don haka hukumar Zata Kara Kaimi akan ayyukan Da suka shafi hajji.

Mallam abba saidu sufi yace tun daga matakin bitar alhazai har Zuwa sansanin alhazai da kuma filin sauka da tashi na jiragen sama hukumar na gudanar da aiki kamar yadda ta saba.

Babban darakta mai barin gado yace dakarun hukumar suna yin hidima tun daga nan gida kano har zuwa Kasa Mai tsarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: