Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na shirin gina katafariyar kasuwar siyar da magunguna a jihar.

Yayin ziyarar duba aiki a sabuwar kasuwara ke Ɗangwauro Gwamna Ganduje ya ce an yi hakan ne da nufin tsaftace sana ar tare da rage yawan shigo da kwayoyin da hukuma ba ta aminta da su ba.
Cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar, Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwuwa don ganin an daƙile ɗabi ar sha ɗmda fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Ya ce kasuwar za ta kasance ƙarƙashin kulawar hukumomin da abin ya shafa ciki kuwa har da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA.
