Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu ya koka kan yadda suke wahala wajen dawo da Kudaden da aka boye a Kasashen waje Wanda wasu shuwagabannin suka boye.

Magu ya kuma yi Roko ga hukumomi da suke da Ruwa da tsaki na duniya dasu taimakawa hukumar akan hanyoyin da za’abi wajen dawo da Kudaden gida Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Mista Tony Orilade ya fitar a jiya cewa na cikin damuwa kan Rashin dawo da Kudaden.

A cewar Magu hanyoyin da ake bi wajen dawo da Kudaden da aka boye su a Kasashen waje suna da Wahala matuka.
Wannan yasa dole su nemi sabbin dabaru wajen ganin An dawo da Kudaden.

Leave a Reply

%d bloggers like this: