Babbar kotun jiha ƙarƙashin mai shari a Justice Dije abdu Aboki ta bada umarnin rataye wani Umar Yakubu Baban Mage mazaunin unguwar Tukuntawa a Kano.

Kotu na tuhumar Baban mage bisa kashe wani Ibrahim Adamu ta hanyar caka masa almakashi.

Tun bayan da kotu ta buƙaci kwarraran shaidu bayan da gwamnatin jihar Kano ta yi ƙararsa bisa zargin, lauyan gwamnati Lamiɗo Soron ɗinki ya gabatar da shaidu shida kuma kotun ta amince da shi.

Yayin karanta hukuncin Justice Dije Abdu Aboki ta ce hukuncin kisa babban laifi ne kuma ya saɓa da sashe na 221 cikin baka.

Sannan ta zartas da hukuncin kisan ta hanyar rataya kamar yadda ta bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: