Rundunar yan Sandan Jihar Kano ta lura da cewa wasu daga cikin masu tuka Babur din Adaidaita sahu suna tukin ganganci akan manyan hanyoyi da kuma titunan unguwanni na birnin Kano da kewaye, inda suke haddasa hadura a kan Titina.

Cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar yansandan jihar Kano DSP Haruna Abdullahi ya rabawa manema labarai,a madadin Kwamishinan yanda sandan jihar Kano Ahmad Iliyas yace wajibi ne duk masu Adaidaita sahu da su ya daura lambar abin hawansu da ta *KAROTA* a jikin mashin dinsa.
Haka zalika Duk Wanda aka kama yana daukar fasinja a gefen Adaidaita sahunsa, ko tuki ba tare da cikakkiyar sheda a jikin babur din saba jami’an yan Sanda zasu kamashi kuma a gurfanar dashi a gaban kuliya.

Wannan wani yunkuri ne da Rundunar yansanda ta keyi na kare lafiya da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano baki daya.
Daga karshe Kwamishinan yan sandan Kano yayi Kira tare da bada sharawa da Al’umma su kauracewa duk wani mai Babur daya dau fasinja a gaba ko kuma bashi da cikakkiyar lambar tantacewa ta hukumarKAROTA.

PR/Police

Leave a Reply

%d bloggers like this: