Tsohon mataimakin shugaban kasar najeriya kuma Dan takarar shugabancin kasar nan a inuwar jami’ar PDP Atiku Abubakar shine ya bayyana hakan.

Inda ya ce Nijeriya tana shiga matsanancin talauci, ga cin hanci da kuma kin gaskiya duk a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan furuci ya fito ne ta Bakin mai taimakawa Atikun akan kafafen yada labarai Mr Paul Ibe ta cikin wata takarda da ya fitar aka rabawa manema labarai a yau
inda yace yan Nijeriya suna rayuwa cikin matsanancin talauci tun daga ranar da Buhari ya zama shugaban kasa a shekarar 2015 har zuwa yau.
Atiku ya ce rahoton Majalisar Dinkin Duniya ne ya kara fadakar da ‘yan Nijeriya kan irin gararin da suke ciki saboda yadda gwamnatin Buhari ta nuna gazawa wurin gyara tattalin arzikin kasar.
Rahoton ya bayyana cewa akwai ‘yan Nijeriya miliyan 98 da ke rayuwa cikin matsanancin talauci. ya kuma nuna mamakinsa matuka kan yadda gwamnatin Buhari ta yi na nuna rashin damuwa da wannan rahoto na majalisar dinkin duniya ta fitar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: