Rundunar yansandan jihar Legas sun cafke wasu matasa dake Shirin tara Yara Kimanin Miliyan daya don shiga kungiyar Tsafi.

Kakakin Rundunar yansandan jihar Bala Elkana shine ya tabbatar kame matasan masu karancin shekaru da makamai irin na gargijiya a hannun yaran da basu wuce 18- 23 ba.
Elkana ya kuma kara da cewa sun cafke Wanda ake zargi da Assasa kungiyar mai suna Yusif Abu dan shekaru 20 a duniya.

Runduna yansandan ta bayyana sunayen Wanda aka kame su takwas kamar haka:

Gabriel, Rilwanu Dauda, Muhammad Sikiru, da oladimeji sai Rasheed Alabi, da Habeeb Idowu, sauran sun hada da mata Olaila Bisola, da hazzan Hawawu.
Dukkanin su basu wuce shekaru 20 ba.
Tunu dai Rundunar ta soma Bincike akansu daga bisani a Mika su gaban Kotu.