“Shi yakemin komai shara, wanki da wanke wanke shi yake ba ya iya jayayya da ni”

Kotun shari ar musulunci da ke Fujairah ta saurari ƙorafin wata mata da ta buƙaci kotun ta raba aurensu da mai gidanta sakamakon tsananin sonta da kulawar da yake bata ya yi yawa.

“Ba ya iya jayayya da ni, shi yake yin girki ya yi shara da wanki sannan yana bani kulawa da yawa”  Inji matar.

A nasa ɓangaren kuwa magidancin ya roƙi kotu da ta bawa matar shawara don ganin ta janye ƙarar.

Daga ƙarshe dai kotun ta ɗage sauraren ƙarar don bawa ma auratan dama ko za au sasanta a tsakaninsu.

Mujallar matashiya ta yi nazarin hakan ba ta taɓa faruwa a yankin Africa ba musamman a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: