Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki shiyyar Kano, Jigawa da Katsina ya ce yanin damuna da marka marka ne ya kawo ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a shiyyoyin.

Kakakin kamfanin na shiyyar Ibrahim Sani ne ya shaida hakan yayin da yake zantawa da ƴan jaridu bisa babban kamfanin raraba hasken Lantarki a Najeriya ya zargi kamfanin Kedco da maƙale wutar lantarkin.

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon tsarin karɓa karɓa da kamfanin suke yi a tsakaninsu.

Kamfanin ya buƙaci abokan hulɗarsa da su ƙara haƙuri zuwa bayan Damuna sannan wutar za ta daidaita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: