Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa kwamitin da aka ɗorawa alhakin tsara Ruga a jihar kano.

Ganduje ya miƙa jinjinar yayin da kwamitin ya kai rahotonsa ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamishin Dakta Jibrila Mohammed.

Cikin dajin da aka duba yuwuwar hakan sun haɗa da ƙananan hukumomi biya kamar haka, Ajingi, Gaya, Bichi, Makoɗa, da Doguwa.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya sha alwashin ƙaddamar da shirin nan ba da jimawa ba