Hukumar yan sandan jihar legas ta cafke wani matashi mai shekaru 29 bisa zargin sa da sojan gona da yake yi yana Kiran kansa a matsayin jami’in Hukumar EFCC.

Matashin da ake zargi mai suna Emeka Emmanuel an kamashi ne a jihar legas Wanda yanzu haka yana tsare a Ofishin yansandan dake unguwar Ojo.

Kakakin Rundunar yansandan jihar legas Bala El-kana ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya.

Inda yace matashin ana zargin sa ne da damfarar mutane ta hanyar cewa zai nemo musu aiki a hukumar EFCC Wanda kuma yake karbar makudan kudade a hannunsu.

An kama Emeka ne da takardar shaidar Aiki na hukumar EFCC na Jabu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: