Shugaban hukumar tace finafinai da ɗab i ta jihar Kano Mallam Isma ila Na abba Afakallahu ne ya jaddada hakan yaƴin wata zantawa da mujallar Matashiya ta yi da shi a ofishinsa.

Bisa sabbin tsarin da hukumar ta ɗakko na ganin cewa an magance matsalar rashin tsarin sanin adadin mutanen da ke cikin masana antar Kannywood.

Afakallahu ya ce babu wani mahaluki da zai shigo masana antar jihar Kano, ba tare da ya yi biyayya ga hukumar tace fina finai ba.

A cewarsa hakan ne zai bada damar cin moriyar cigaban da suke ƙoƙarin kawowa masana antar tare da rage yin fina finan da ke ɓata tarbiyya.

Sannan yana fata waɗanda suka jahilci tsarin da su biyo sahu don ganin an gudu tare an tsira tare.

Ya ƙara da cewa, akwai shiri na musamman ga mutane na ƙasa musamman waɗanda suka kasance farin shiga sannan waɗanda suka kasance cikin harkar tun tuni za su ci moriyar wani bashi mai tsoka da gwamnati za ta bayar don bunƙasa sana ar tasu.

Sannan ya yi kira ga al ummar jihar Kano da su kasance cikin shirin ganin sabon sauyin da za su kawo musamman a fanni daban daban don ganin an ƙayatar da su a bisa abinda suke burin gani ba tare da lalata tarbiyya ba.

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar a gobe da misalin ƙarfe 7:00pm na yamma a shafinmu na youtube.

Leave a Reply

%d bloggers like this: