Babbar Kotun majistiret dake jihar katsina karkashin mai shari’a hajiya Fadila Dikko ta bada umarnin cigaba da tsare wani mutum Mai shekaru 40 Mai suna Abubkar Bala a gidan yari bisa zargin sa da Mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da sauran manyan Laifuka da suka hada da fashi da garkuwa da mutane.

Mai Shari’a fadila ta bada umarnin cigaba da tsare shi ne har sai har sai ranar 10 ga watan Oktoban wannan shekara.

Da yake jawabi Dan sanda Mai gabatar da kara Sergent Lawal Bello ya bayyana wa kotu cewa Wanda ake zargi an kamashi ne a garin Labo dake Karamar hukumar Batsari a gidan wani da ake zargi cewa dan fashi da makami ne Mai suna bello Dogo Wanda yayi k’aurin suna akan satar mutane da da fashi da makami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: