Connect with us

Labarai

Fim da waƙa halak ne kuma jihadi ne idan an bi tsarin musulunci masu yi za su samu ɗumbin lada mara iyaka – Shek Moriki

Published

on

Babban malami a hukumar Hizbah ta jihar Kano Shek Muhammad Tukur moriki Rijiyar Lemo ne ya bayyana haka cikin wani shirin mai suna Rabin Ilimi da ake gabatarwa a Mujallar Matashiya.

Malamin ya ce yin fim ko waƙa ya halatta kuma jihadi ne sannan ak2f ɗumbin lada mai tarin yawa ga wanɗanda ke yin sana ar tasu.

Malamin ya ƙara da cewa matuƙar an gina fim ɗin ko waƙar bisa tsari da koyarwar addinin musulunci to kuwa babu shakka masu yi na kwankwaɗar lada musamman idan suka aike da saƙo mai muhimmanci ga jama a.

Amma akasin hakan kuwa babu abinda zai haifar illa samun zunubi matuƙar ba a gina abin bisa koyarwa ta addinin musulunci ba.

Shek Moriki ya ce ko a zamanin Annabi S.A.W ma an yi waƙe wanda hakan ke nuni da cewa abin ya samo asali.

Amma yin bambaɗanci ko ƙarin gishiri a cikin waƙar haramun ne, inji shek Moriki.

Idan ba ku manta ba kuma a baya bayannnan ma mujallar Matashiya ta tattauna da shugaban hukumar tace fina finai da ɗab’i ta jihar kano Mallam Isma ila Na abba Afakallahu wanda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an tsaftace sana ar tare da karkaɗe bara gurbin ƴan masana antar.

Cikin tsarin da suke kuwa shi ne yin rijinta na kowanme fanni matuƙar mutum zai taka rawa a cikin sana ar hatta ɗan aike.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Sama Da Mutane 85 cikin 100 Na Amfana Da Tallafin Wutar Lantarki

Published

on

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Ministan ya ce sama da Naira tiriliyan 1 da za a samu sakamakon janye tallafin wutar lantarki, za a yi amfani da su wajen inganta samar wutar lantarki da ayyukan more rayuwa a ƙasar nan.

 

Jaridar The Nation ta ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin ‘Hannu da Yawa’ na Rediyo Najeriya da ke Kaduna.

 

Ministan ya ce wasu ƴan tsiraru masu hannu da shuni da kamfanoni ne kawai ke kwashe garaɓasar tallafin wutar lantarkin.

 

A cewarsa kaso 40% na tallafin wutar lantarkin yana amfanar kaso 15% da ke samun wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kowace rana.

 

Idris ya jaddada cewa har yanzu kaso 85% cikin 100% na al’ummar da suke ƙarƙashin sauran rukunonin wutar lantarkin na samun tallafi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano Ya Nuna Bacin Rai Kan Sakin Yan Daba A Kano

Published

on

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki ‘yan daba da ke kulle a jihar.

Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar.

Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati.

Ya bayyana yawan ‘yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin kubutar da ‘yan dabar domin biyan buƙatar kansu ta siyasa.

Continue Reading

Labarai

Jagororin APC A Ondo Sun Zargi Gwamnan Jihar Da Yin Makarkashiya A Zaben Fidda Gwani

Published

on

Wasu jagororin jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun zargi gwamnan Jihar Lucky Ayedatiwa akan kulla makarkashiya akan zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Afrilu da muke ciki.

 

 

 

Jagororin jam’iyyar karkashin wata kungiya mai rajin tabbatar da shugaban nagari a Jihar sun ce gwamnan na kokari sauya zaben na fidda gwani.

 

 

 

Shugaban kungiyar Evangelist Tade Ojo ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa da shugaban kasa Bola Tinubu kan lamarin.

 

 

 

Shugaban ya ce gwamnan tare da magoya bayansa sun buga katuna da tambarin jam’iyyar su na rabawa mutanen da ba mambobin jam’iyyar ba.

 

 

 

Shugaban ya bukaci jam’iyyar APC ta kasa da shugaban kasa Tinubu da su dakatar da Ayedatiwa akan yunkurin tarwatsa zaben na fidda gwani.

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: