Wani Mutum ya yanke jiki ya fadi nan take ya mutu.

Lamarin ya faru ne a jihar legas inda wani Mutum Mai suna Jude Oladapo ya yanke jiki a filin tashi da sauka na jirgin sama Na Murtala Muhammad dake legas.

Oladapo dan shekrau 44 yaje filin jirgin saman ne da niyyar tafiya kasar Faransa anan aka sanar dashi mutuwar matarsa ta hanyar wayar tafi da gidanka, inda Shima nan take yace fa garinku.

Mai magana da yawun Rundunar yansandan jihar legas dake Filin jirgin sama DSP Joseph Alabi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa abin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin jiya.
Tuni dai likitoci suka tabbatar da mutuwar Oladapo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: