Wasan Hausa da waƙar da za su taimaki musulunci da musulmi ne kaɗai ya halatta ba shiririta ba, Duk waƙa ko wasan Hausar da ba zai taimaki musulunci da musulmi ba haramun ne inji shek Moriki

Babban malami a Hukumar Hizba ya jaddada fatawar da ya bayar na cewa ya halatta a yi wasan Hausa da waƙar da za su taimaki addinin musulunci da musulmi.

Malamin da wasu ke ɓatanci a kansa bisa fatawar da ya bayar, ya barranta kansa da cewa wasu ɓata gari ke masa ɓatanci wasu kuwa akasin fahimta ne.

Shek Moriki ya bayar da fatawar ne cikin wani shiri da ake gabatarwa na Rabin Ilimi a Mujallar Matashiya.

Wanda daga baya wasu ke sukar fatawar, malamin ya ce muddin aka yi wasan Hausa ko waƙar da ta saɓawa addini to haramun ne aikatata ƙarara musamman abinda zai rusa tarbiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: