Za a rufe gidajen man ne saboda tsangwamar masu gidan mai da ake yi kan gina gidajen mai, kuma majalisa ta ƙi yin gyara kan dokar.

Cikin wata sanarwa da shugaban masu siyar da man fetur a Najeriya reshen jihar Kano Bashir Ahmad Ɗan malam ya rattaɓawa hannu, ya umarci dukkanin gidajen mai masu zaman kansu su rufe gidan man har sai buƙatarsu ta biya.

Bayan zaman da suka gudanar na masu ruwa da tsaki a ƙungiyar daga ƙarshe dai sun cimma matsayar rufe gidajen man fetur a Kano baki ɗaya.

Sanadin kuwa bai wuce yadda ake tatsar haraji daga gurinau kuma ake tsangwamarsu bisa yadda suke gina gidajen mai a Kano ba

#MujallarMatashiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: