Jarumin fim ɗin Hausa Adam Zango ya ɗauki nauyin karatun mutum 101 a makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zaria.
Adam Zango da ya kasance shugaban kamfanin Prince Zango Nig LTD ya kashe tsabar kuɗi naira miliyan 46.75.
Jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa yayi matuƙar godiya da amfani da damar da ya samu wajen tallafawa na ƙasa.
Makarantar ta kasance ta masu hannu da shuni yayinda shugaban makarantar Mallam Hamza Jibril ya tabbatar da hakan har ma suka miƙawa jarumin takardar ban girma dangane da lamarin.